1=Ba zaka iya kallon bidiyo da wayar salularka ba in dai ta China ce sabo da rashin ingancin tsarin kallo ta intanet 2=Ba zaka iya sauraron BBC ko Muryar Amerika ba a daidai lokacin da suke gabatar da shirin muddin ba salula sumfurin pocket pc ko windows mobile gareka ba. 3=Za ka iya dauko murya ta sumfurin mp3 na takaitattun labaru na BBC ko cikakken shirin BBC ko Muryar Amerika.Da farko dai idan ka shiga tashar BBC ko Muryar Amerika,sai ka latsa inda ka ga an ce saurari labarun mu,sai ka latsa inda ka ga an sa labaru mp3.Sai ka danna inda aka ce download,wannan tsarin zai kai ka mahajar aje muryar wayar ka watau music,wanda yake bayan ka dauko shirin,zaka iya samun labarun a cikin music ko audio na wayar ka. 4=kada ka fara sa adireshin yanar gizo a wayar ka da ya fara da WWW,matsawar wayar salular ka ta China ce.Saboda matsawar ka nemi shiga irin wayannan shafukan,zasu ce kwakwalwar wayar ka yayi kadan watau not enough memory. 5=Zaka iya shiga shafin ka na facebook,matsawar dama ka yi rajista da su,in kuwa ba haka ba,sai ka je www.facebook.com a komputar yanar gizo,bayan ka yi rajista sai ka zo a wayar ka na salula ka sa wannan bayanin domin shiga shafin facebook da salular ka.

:=:

Hindi Song
Download Android App for Free
Phone  IMO  9Apps  more